• Home  
  • An Sauyawa Karar Dambarwar Wasu Filaye A Rijiyar Zaki Kotu .
- Babban Labari - Labarai

An Sauyawa Karar Dambarwar Wasu Filaye A Rijiyar Zaki Kotu .

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 1 karkashin jagorancin mai shari’a,Justice Dije Audu Aboki, ta ci gaba da sauraren shari’arnan da aka shigar gaban ta, kan dambarwar wasu filaye, a yankin unguwar Rijiyar Zaki. Sai dai kotun ta sauya kotun da za ci gaba da sauraren karar, zuwa wata babbar kotun jiha dake zamanta a […]

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 1 karkashin jagorancin mai shari’a,Justice Dije Audu Aboki, ta ci gaba da sauraren shari’arnan da aka shigar gaban ta, kan dambarwar wasu filaye, a yankin unguwar Rijiyar Zaki.

Sai dai kotun ta sauya kotun da za ci gaba da sauraren karar, zuwa wata babbar kotun jiha dake zamanta a unguwar Miller road Kano.

Lauyan masu karar Barista Jonathan , ya shaidawa kotun cewa wanda yake karewa suna da dukkan takaddun mallakar filayen, amma suna zargin kwamishinan kas ana jihar Kano, ya bayyana musu cewa takaddunsu tamkar takaddar tsirece don haka suke neman kotun ta yi musu adalici.

Anasa bangaren lauyan gwamnatin da kwamishinan shari’a da kuma kwamishinan kasa da aka yi karasu a gaban kotun ya soki rokon lauyan masu karar kan wasu takaddu da suka gabatarwa kotun.

Lauyan masu kara ya ce ,dukkan wadanda yake tsayawa duk sun bayyana a gaban kotun, kuma za su iya bakin kokarinsu wajen nema musu hakkinsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai