Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun miƙa ta’aziyyarsu ga tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza.
Hajiya Hadiza ta rasu ne a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci bayan gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya isar da saƙon ta’aziyyar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na Harkokin Yaɗa Labarai na gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, shugaban NSGF ya bayyana rasuwar a matsayin rashi mai raɗaɗi da girma, ba ga iyali kaɗai ba har ma da duk waɗanda suka san marigayiyar.
Ya ce marigayiyar ta rayu rayuwa mai cike da tawali’u, karamci da kuma sadaukarwa ga kyawawan ɗabi’un iyali, yana mai cewa rasuwarta ta haifar da babban giɓi a rayuwar waɗanda ta bari.
Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci iyalan mamaciyar da su yi haƙuri tare da ɗaukar darasi daga kyakkyawar rayuwar da ta yi da kuma kyakkyawan gadon da ta bari na alheri, imani da tausayi.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga Farfesa Jega, ’ya’yansa da dukkan iyalai, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi.
Haka kuma, gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar, Ya karɓi ayyukanta na alheri a matsayin ibada, tare da sanya ta a Aljannatul Firdaus.
Rasuwar Hajiya Hadiza Jega ta ci gaba da jawo saƙonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar, inda mutane da dama ke yabon kyawawan halayenta da gudummawar da ta bayar ga iyali da al’umma.

