Iran ta yi gargaɗin cewa muddin Shugaba Trump, ya ci gaba tare da aiwatar da barazanarsa ta kai hari kan wuraren farar hula da suka hada da gadoji da tasoshin wutar lantarki, to shakka babu ramuwar-gayya da za ta yi za ta kasance mummunar gaske kuma ba ƙarama ba.
Yau ne ya kamata ya zama ƙarshen wa’adin da Shugaba Trump ya ɗeba wa Iran ta buɗe mashigar Hormuz, ko ta fuskanci munanan hare-hare na lalata kayayyakinta da ba na soji ba – ciki har da tashoshin samar da lantarki.
A ranar Lahadi ne, shugaban na Amurka ya kara sanya sabon wa’adi na zuwa gobe Talata, ga Iran ɗin ta sake buɗe mashigar.
Kafofin yaɗa labarai na Amurka na cewa masu shiga tsakani – na can suna ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta tsawon kwana 45 – kodayake rahotanni na cewa ba lalle a samu nasarar hakan ba.
A dalilin sabuwar barazanar ta Trump, farashin mai ya yi sama a Asia a yau Litinin, amma kuma kasuwannin hannun jari na nan yadda suke – ba su tashi ba, kuma ba su yi kasa ba.

