Gobara ta tashi a Kwalejin Koyon Aikin Lafiya da Ungozoma ta Jahun a Jihar Jigawa a daren jiya Talata.
Lamarin da ya jefa ɗalibai da ma’aikata cikin fargaba da tashin hankali.
Rahotanni sun nuna cewa wutar ta taso ne daga wani ɗaki kafin daga bisani ta bazu zuwa wasu sassan gine-ginen makarantar.
Ɗalibai da ma’aikata sun yi ƙoƙarin tsira rayukansu da kwashe wasu kayayyakinsu kafin isowar jami’an kashe gobara.
Sai dai duk da haka, gobarar ta lalata kayan karatu da wasu muhimman abubuwa da dama.
Jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan wutar tare da hana ta ƙara yaɗuwa zuwa sauran gine-gine.
A halin yanzu, hukumomi sun fara bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

