Al’ummar karamar hukumar Bichi sun shirya gagarumin bikin bankwana da tsohon area kwamanda na yankin Bichi, ACP Dahiru Yusuf Alkali, bayan ya kammala aikinsa da rundunar ƴan sandan Najeriya.
Bikin karramawar ya samu halartar manyan baki da suka hada da shugabannin al’umma, masu rike da sarautun gargajiya da jami’an tsaro, da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban.
A jawabansu dabam-daban mahalarta bikin karramawar sun yaba wa ACP Dahiru Yusuf Alkali bisa gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma ƙulla kyakkyawar alaka tsakaninsa da al’ummar yankin Bichi.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa ACP Dahiru Yusuf Alkali, bisa jajircewa da nuna ƙwarewa da kuma rikon amanar da ya nuna a tsawon shekarun da ya yi yana hidimtawa kasa.
Ya ce irin kwazo da jajircewar da ACP Alkali, sun taimaka matuka wajen inganta harkokin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a shiyar Bichi.
CP Bakori ya kuma yi masa fatan alheri da samun ci gaba a rayuwarsa ta gaba bayan ritaya daga aikin ɗan sanda.
A nasa jawabin, ACP Dahiru Yusuf Alkali ya nuna matukar godiyarsa ga al’ummar Bichi bisa girmamawa da kaunar da suka nuna masa, yana mai cewa ba zai manta da irin hadin kai da goyon bayan da ya samu daga jama’a da sauran jami’an tsaro ba a lokacin da yake bakin da aikinsa.
A ƙarshe an kammala bikin da bayar da kyautuka ga ACP Dahiru Yusuf Alkali, tare da yi masa fatan alkairi.

