Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta yi kira ga ma’aikatan ma’aikatar kuɗi da su rinka mutunta alamomin ƙasa Najeriya a matsayin muhimmin nauyin ƙasa da ya rataya a wuyansu.
Darakta Janar na hukumar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai da aka shirya wa ma’aikatan ma’aikatar a Abuja, domin ƙarfafa fahimta kan muhimmancin alamomin ƙasa da kuma dabi’un kasa.
Mallam Issa-Onilu ya bayyana cewa alamomin ƙasa kamar tuta da taken ƙasa suna wakiltar haɗin kan Najeriya da martabarta, don haka ya zama wajibi ga kowane ɗan ƙasa ya mutunta su tare da amfani da su yadda ya dace.
Ya kuma ƙara da cewa Kundin dabi’un kasa an tsara shi ne domin ƙarfafa kishin ƙasa da fayyace nauyin da ke kan gwamnati da kuma al’umma wajen gina Najeriya mai ci gaba.
A nasa jawabin, Ministan kuɗi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya yaba wa NOA bisa ƙoƙarinta na bunƙasa kishin ƙasa da inganta kyawawan ɗabi’u.
Ya ce ma’aikatar za ta naɗa jami’ai da za su jagoranci wayar da kan ma’aikata kan mutunta alamomin ƙasa, tare da ci gaba da haɗa gwiwa da NOA wajen faɗaɗa wayar da kan jama’a.
A yayin taron, an kuma koyar da mahalarta yadda ake rera taken ƙasa yadda ya kamata, da kuma yadda ake amfani da tutar Najeriya da sauran alamomin ƙasa bisa ƙa’ida.

