Kotun majistare mai lamba 53 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Jamilu Ɗayyabu Haruna, ta fara sauraron ƙarar da ’yan sanda suka shigar kan wani mutum mai suna Musa Adamu, wanda ake zargi da laifin sojan gona da cuta.
A cewar ƙunshin tuhumar, ana zargin Musa Adamu da yin sojan gona da sunan cewa shi babban jami’in ’yan sanda ne mai muƙamin CSP, tare da karɓar kuɗi daga hannun wasu mutane bisa zargin cewa zai taimaka musu wajen samun aikin dan sanda.
A zaman kotun da aka gudanar ranar Alhamis 10 ga Satumba 2026, an karanta wa wanda ake tuhuma ƙunshin zarge-zargen da ake yi masa, amma ya musanta aikata laifukan.
Kotun ta bayar da belinsa, da sharadin cewa zai kawo wanda zai tsaya masa mai matakin albashi na 15, sannan idan ya tsere, za a biya tarar Naira dubu dari biyar.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba 2026.
