• Home  
  • AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.
- Labarai

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Mataimakin sufeto janar na yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya Zone One Kano, AIG Garba Ahmed, ya bukaci daliban farko da suka kammala karatu a makarantar sakandaren yan sanda da ke Dawakin Kudu su kasance masu ladabi, gaskiya, kishin kasa da kuma rikon amana. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar shiya ta […]

Mataimakin sufeto janar na yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya Zone One Kano, AIG Garba Ahmed, ya bukaci daliban farko da suka kammala karatu a makarantar sakandaren yan sanda da ke Dawakin Kudu su kasance masu ladabi, gaskiya, kishin kasa da kuma rikon amana.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar shiya ta ɗaya, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sanarwar, AIG Garba Ahmed ya bayyana kammala karatun daliban a matsayin wani muhimmin tarihi na ci gaban makarantar, yana mai cewa kasancewarsu daliban farko, nauyi akansu na kare martaba da kimar makarantar ta hanyar nuna kyawawan halaye.

Ya ce daliban su ci gaba da kasancewa jakadu nagari ta hanyar riko da gaskiya da jajircewa da kuma nuna kishin kasa a duk inda suka samu kansu.

AIG Garba Ahmed, ya kuma yabawa babban Sufeto janar na yan sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu,bisa jajircewarsa wajen bunkasa harkar ilimi a cikin rundunar yan sandan Najeriya.

Haka kuma, ya taya iyayen daliban da masu kula da su da malamai da ma’aikatan makarantar murna bisa irin kokari da gudummawar da suka bayar wajen ganin an samu nasara.

A karshe, AIG Garba Ahmed ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban kasa, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa makarantar domin samar da dalibai masu nagarta da kyakkyawar tarbiyya.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000