• Home  
  • Kwamandan NSCDC ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Dry Port Kan inganta tsaro.
- Labarai

Kwamandan NSCDC ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Dry Port Kan inganta tsaro.

Kwamandan hukumar tsaron civil defense reshen jihar Kano, Muhammad Hassan Agalama, IION, ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port a Kano, inda suka tattauna hanyoyin ƙara inganta tsaro da kare tashar daga duk wata barazana. Ganawar, wadda aka gudanar a ofishin kwamandan a cikin makon nan, ta mayar da hankali ne kan muhimmancin […]

Kwamandan hukumar tsaron civil defense reshen jihar Kano, Muhammad Hassan Agalama, IION, ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port a Kano, inda suka tattauna hanyoyin ƙara inganta tsaro da kare tashar daga duk wata barazana.

Ganawar, wadda aka gudanar a ofishin kwamandan a cikin makon nan, ta mayar da hankali ne kan muhimmancin samar da ingantaccen tsaro a tashar Dala Inland Dry Port, kasancewar tashar na daga cikin muhimman cibiyoyin da ke da alaƙa da harkokin kasuwanci da sufuri.

A yayin ganawar, an tattauna matakan da za a ɗauka domin ƙarfafa kariyar muhimman kadarori da ababen more rayuwa da ke tashar, tare da inganta hanyoyin musayar bayanan sirri tsakanin jami’an tsaro da mahukuntan tashar.

Dala Inland Dry Port na da muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa harkokin shigo da fitar da kaya, lamarin da ya sa ake kallon tsaron tashar a matsayin wani muhimmin al’amari da ya shafi harkokin tattalin arziki da tsaron ƙasa.

Hukumomin biyu sun jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da musayar bayanai wajen gano tare da dakile barazanar tsaro, musamman a wuraren da ke da muhimmanci ga harkokin kasuwanci da ci gaban ƙasa.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai