Kotun shari’ar addinin musulunci dake zamanta a unguwar Jogana Kano, karkashin jagorancin mai shari’a, Kamalu Haruna, ta bayar da umarnin tsare mutanen da ake zargi da hada kai da yunkurin aikata tsafi.
Wadanda ake tuhumar sun hada da, Yusuf Mahmud mazaunin Rano, Abdurraham Abbas mazaunin Kwasamgwami Gezawa da Sha’aibu Yawale Daganawa Bunkure da Abubakar Iliyasu Zangon Dakata da kuma Ishaq Isah Rano.
Bayan karanta musu ƙunshin tuhumar, dukkansu sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.
Lauyan gwamnatin jihar Kano, ya roki kotun ta basu wata rana, Inda kotun ta sanya ranar 14 ga watan Satumba 2026 domin yanke musu hukunci.
Sakamakon rashin bashi kudin ne yaje ofishin yan sandan Rano, ya shigar da korafi har
Tunda farko ana zargin daya daga cikin mutanen mai suna, Yusuf Mahmud Rano da yanke yatsan sa da wuka , bayan an tallata masa cewar za a bashi naira miliyan 80 idan ya kawo.
Daganan jami’an yan sanda suka fara gudanar da bincike har suka kamo sauran mutanen, tare da gano wukar da aka yi amfani da ita da kuma yatsan da aka yanke.
