Jami’ai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce barkewar cutar Ebola ta bazu zuwa wani lardi, wanda shi ne na bakwai. Gwamnan Sud-Ubangi ya ce an tabbatar da samun cutar a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Kongo.
An yi imanin cewa majinyacin ya bi ta wasu larduna da dama, ciki har da wasu wuraren da ba a tabbatar da samun cutar ba.
Sud-Ubangi ba shi da iyaka da ko ɗaya daga cikin wuraren da cutar ta riga ta shafa. An samu rahoton sama da mutum 6,000 da suka kamu da cutar a wannan zagayen ɓarkewar, ciki har da sama da mutum 3,000 da suka mutu.
