Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato nau’in ƙwayoyi daban-daban har guda 5,916 da kuma kunshin tabar wiwi guda biyar.
Kamen dai ya biyo bayan wasu samame na musamman da rundunar ta gudanar bisa bayanan sirri a wurare daban-daban na jihar, domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Tijjani Murtala.
A cewar sanarwar, rundunar ta gudanar da samamen ne a yankunan rundunonin ’yan sanda na Kazaure da Gumel da Miga da Dutse, Sundumina da Taura da Babura da Ringim da Sara da kuma Aujara.
Rundunar ta ce, jami’anta sun ƙwato jimillar ƙwayoyi da miyagun abubuwa 5,916, da kuma tubalan tabar wiwi guda biyar daga hannun waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da wuraren da ake rarraba su.
Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai: Exol, Tramadol, D5, Diazepam, Taramol, Rubber Solution, Pregabalin da tabar wiwi da sauran nau’o’in miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka kama sun haɗa da: Yahaya Ibrahim, mai shekara 35, mazaunin ƙauyen Darai da ke ƙaramar Hukumar Jahun; Adamu Ya’u, mai shekaru 33, daga ƙauyen Jamaga a ƙaramar Hukumar Miga; da Musa Musa, mai shekara 22, wanda aka fi sani da Alili Boss, daga Nasarawa Jalo ƙuarters a Gumel.
Sauran sun haɗa da: Sani Kabiru, mai shekara 35, daga ƙaramar Hukumar Ingawa ta Jihar Katsina; Hashimu Haladu, mai shekara 40, daga ƙauyen Nafara, Sundumina, ƙaramar hukumar Birnin Kudu; Mustapha Kabiru, mai shekara 22, daga Katutu Quarters, Ringim; da Sani Harisu, mai shekara 25, daga Tsangaya ƙuarters, garin Sara a ƙaramar hukumar Gwaram.
Rundunar ta ce, an gudanar da binciken farko kan waɗanda ake zargin, sannan aka gurfanar da su gaban kotunan da suka dace domin fuskantar shari’a bisa tanadin doka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen bisa jajircewarsu da kuma ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye a jihar.
