• Home  
  • Rundunar yan sandan Kano ta kama mutane 10 da ake zargi da satar motoci tsakanin jihohi.
- Labarai

Rundunar yan sandan Kano ta kama mutane 10 da ake zargi da satar motoci tsakanin jihohi.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane goma da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar da ke satar motoci tare da kai su jihohi daban-daban domin sayarwa. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a area command ta […]

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane goma da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar da ke satar motoci tare da kai su jihohi daban-daban domin sayarwa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a area command ta rTarauni, Kano.

Ya ce jami’an Special Intervention Squad sun fara kama mutum biyar a jihar Adamawa a ranar 7 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri.

A cewarsa, an samu wata motar Mercedes Benz GLK 350 a hannun waɗanda aka kama.

Binciken da rundunar ta gudanar daga bisani ya kai ga gano wasu motoci goma da ake danganta su da ƙungiyar a wurare daban-daban a Kano da jihohin makwabta.

Kwamishinan ya ce a ranar 12 ga Satumba, jami’an rundunar sun kuma kama wasu mutane biyar a Kwankwasiyya City Kano, inda suka same su da wata Toyota Hilux da aka ce an sata.

Ya ce hakan ya sa adadin waɗanda aka kama ya kai goma, yayin da motocin da aka kwato suka kai goma sha biyu.

A cewar kwamishinan, waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata satar motoci a Kano, Katsina, Bauchi, Gombe da wasu jihohin makwabta.

Ya ce ana ci gaba da bincike, yayin da rundunar ke ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi da tserewa.

Rundunar ta kuma ce 11 daga cikin motocin da aka kwato ba su da rajista, abin da ta ce yana wahalar gano ainihin masu motocin.

Ta bukaci masu motocin da aka kwato da su tuntubi rundunar tare da gabatar da shaidar mallakar su.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi na mutane ko motoci da suke zargin na sata ne ga ’yan sanda.

Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai