Wata kotu a Jihar Edo ta yanke wa wasu mutane huɗu hukuncin kisa kan laifuka da dama, bayan samun su da hannu wajen sace wata mata a Kasuwar Kayan Lambu da ke kan titin Airport a birnin Benin.
Mai shari’a Aigbona Momodu na Kotun Hukuna Manyan Laifuka ta Jihar Edo ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, a shari’ar satar mutane ta farko da kotun ta yanke hukunci a kanta.
An gurfanar da mutanen huɗu, da suka hada da Marvellous Isaac, da Wisdom Michael, da Rufus Emete Michael da Gift Raphael ne kan tuhume-tuhume 11 da suka haɗa da satar mutane, da haɗa baki, da fashi da makami, da ayyukan ƙungiyar asiri da kuma mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba.
A yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Momodu ya ce doka ba ta ba shi damar yin sassauci wajen zartar da hukuncin da aka tanada ba.
