• Home  
  • Tarayyar turai ta yaba da shirye-shiryen ’yan sanda Kano gabanin zaɓen 2027.
- Labarai

Tarayyar turai ta yaba da shirye-shiryen ’yan sanda Kano gabanin zaɓen 2027.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar ta shirya tsaf domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan babban zaɓen shekarar 2027. Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar shirin tarayyar turai mai tallafa wa inganta shugabanci da dimokuraɗiyya a Najeriya […]

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar ta shirya tsaf domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan babban zaɓen shekarar 2027.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar shirin tarayyar turai mai tallafa wa inganta shugabanci da dimokuraɗiyya a Najeriya (EU-SDGN), wadda ta kai ziyara hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, ranar 19 ga Oktoba, 2026, domin tantance shirye-shiryen hukumomin tsaro gabanin zaɓen.

A cewar mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shugabar tawagar, Hannan Roberts, ta ce ziyarar na da nufin duba matakan da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka ɗauka, tare da gano wuraren da ake buƙatar ƙarin tallafi domin gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya.

Anasa jawabin kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya ce tun bayan tunda na zo jihar ya mayar da hankali wajen yaƙi da ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan tashin hankali a jihar.

Ya bayyana cewa ƙaddamar da samame na musamman mai suna Operation Kukan Kura, tare da amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukan tsaro, ya taimaka wajen rage ƙarfin masu aikata laifuka da ’yan bangar siyasa.

Kwamishinan ya ƙara tabbatar da cewa rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro ƙarƙashin kwamitin haɗin gwiwa kan tsaron zaɓe domin tabbatar da zaɓe cikin lumana, ’yanci, adalci da sahihanci.

Ya kuma jaddada cewa rundunar za ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa tare da mutunta haƙƙin bil’adama a dukkan matakan zaɓen.

 

A nata ɓangaren, Hannan Roberts ta yaba da matakan tsaron da rundunar ke ɗauka, tare da bayyana gamsuwarta da shirye-shiryen da aka yi zuwa zaɓen 2027.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai