Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kwato wata motar Hyundai, wadda aka sace a harabar Cocin St. Thomas da ke kan titin Airport Road a Kano.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an sace motar ne a ranar 25 ga watan Oktoba, yayin da mai ita, Uchenna Emmanuel, ya je halartar ibadar Lahadi.
Sanarwar ta ce jami’an rundunar sun gano motar a harabar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano a ranar 26 ga watan Oktoba, kafin su kwato ta a ranar 28 ga watan Oktoba tare da miƙa ta ga mai ita.
Rundunar ta shawarci masu motoci da su ƙara sanya matakan tsaro, ciki har da amfani da na’urar bin diddigin mota da makullan kariya.
Ta kuma ce ana ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda ake zargi da satar motar.
