• Home  
  • Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa
- Labarai

Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kano Municipal mai barin gado, Honorabul (Dr) Sha’aban Sharada,

Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kano Municipal mai barin gado, Honorabul (Dr) Sha’aban Sharada, a matsayin Babban Sakataren Zartarwar Hukumar kula da Almajirai da Yara Marasa zuwa Makaranta wanda kudirin kafa Hukumar ya samu sahalewa a 2023.

Sharada ya yi Digirinsa na farko a bangaren aikin aikin Jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester da ke Birtaniya.

Sanarwar nadin ta fito daga Malam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a ranar Lahadi 28, ga Mayun 2023.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000