• Home  
  • Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Bayan Cire Tallafin Man Fetur
- Labarai

Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau a Abuja.

Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce za ta fara yajin aiki na gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan nan na Yuni.

Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau a Abuja.

Daman a yau ne shugabannin suka kira wannan taro domin tattaunawa da bayyana matakin da za su dauka bayan da sabon shugaban kasar ya furta cewa kasar ta janye tallafin mai.

Wannan sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan kasar, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000