Kamfanin man fetur na kasa NNPC ya ce, nan ba da jimawa ba, zai janye daga mallakar da ya yi a kan kayayakin man kasar nan.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin ya rubanya farashin litar man fetur a gidajen mai mallakar kamfanin.
Shugaba kamfanin na NNPC Mele Kyari ya ce, nan ba da dadewa ba farashin zai sauko idan aka sami wasu kamfanoni da za su shiga a dama da su wajen samar da man.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa, gwamnati ta dakatar da tallafin man fetur.
Tun bayan wannan furuci na sabon shugaban ne aka fara samun dogayen layi a gidajen sayar da mai.