• Home  
  • Hukumar KAROTA ta cafke jabun magani na fiye da Naira miliyan 50
- Labarai

Hukumar KAROTA ta cafke jabun magani na fiye da Naira miliyan 50

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta sami nasarar cafke jabun magani na fiye da Naira miliyan 50.

Hukumar Kano KAROTA ta cafke jabun magani na fiye da Naira miliyan 50

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta sami nasarar cafke jabun magani na fiye da Naira miliyan 50.

Hukumar ta sami nasarar cafke jabun maganin ne a kan titin Murtala Mohammed da ke birnin Kano.

Lokacin da direban motar yake ƙoƙarin shiga  kasuwar Sabon Gari domin rabawa a cikin shaguna.

Daga cikin magungunan da aka cafke sun hada da; Maganin ciwon jiki, da maganin zazzaɓi da maganin Tari, da sauransu.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir ya ce Hukumar KAROTA ba za ta zuba ido ta bari ana ta’ammuli da miyagun kwayoyi a jihar Kano ba.

Inda ya ja hankalin al’umma da su guji siyan magani a wajen da bai dace ba, domin guje wa fadawa cikin matsala.

Yace ƙofar Hukumar a buɗe take wajen karɓar bayanin sirri domin daƙile yawaitar jabun magani a faɗin jihar nan baki daya

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai