Aƙalla jiragen fasinja 12 a Turai sun fuskanci tangarɗa

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana jerin barazanar bama-bamai da ke shafar jiragen fasinja a faɗin Turai a matsayin barazanar da ba ta gaske ba, amma ta jaddada cewa ana ɗaukar kowane lamari da muhimmanci.

Aƙalla jirage fasinja goma sha biyu a Turai sun fuskanci tangarɗa sakamakon barazanar cewa an dasa bama-bamai a cikinsu, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu saukar gaggawa a filayen jiragen sama.

Zuwa yanzu dai, ba a gano wani abin fashewa ba. Wata fasinja ke nan take cewa ana tsaka da tafiya lokacin da aka yi barazanar, ba mu san abin da ke faruwa ba.

Jami’an tsaro sun yi saurin fitar da mu daga jirgin ba tare da ɓata lokaci ba.

‘Yan sanda a Jamhuriyar Czech sun ce jirage huɗu sun sauka lafiya a filin jirgin saman Prague. Tun da farko sun samu gargaɗi cewa an dasa abin fashewa a cikin jiragen.

Post masu alaƙa

Ɗan takarar shugaban ƙasa da ya sha kaye a zaɓen Brazil ya tsere zuwa Amurka

Ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia

‘Masar za ta taimaki Saudiyya wajen kariya idan ta buƙaci haka’