Mun yi maraba da hukuncin kotu da ya soke takarar Atiku – Nafi’u Bala

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Hon Nafiu Bala Gombe ya ce ya yi maraba da hukuncin babbar kotun tarayya da ya soke shugabancin David Mark na jam’iyyar.

A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayyar ta yanke hukuncin soke duk matakan da ɓangaren na David Mark ya ɗauka a madadin jam’iyyar.

Matakan sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

Nafi’u Gombe, wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya yi maraba da hukuncin kotun.

”Dama na jima ina magana a kan gaskiya, gaskiya, to ga shi yau gaskiyar ta yi halinta”, in ji shi.

Dama dai Nafi’u Gombe ya tsayar da ƴantakara a ɓangarensa.

”To yanzu za mu mayar da hankali wajen ci gaba da tallata ƴantakararmu domin tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe”, in ji shi.

Post masu alaƙa

Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC

Yan sanda sun kwato motar da aka sace a harabar cocci a kano

Yan sanda da ƙungiyoyi sun wayar da kan matasa kan gudanar da zaɓe cikin lumana a Kano