Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya yi Alla-wadai da hukuncin kotun da aka yanke ranar Alhamis, wanda ke ƙoƙarin ƙwace shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark, yana mai zargin cewa mataki ne na shirin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 saboda shi ɗan Arewa ne.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai da Sadarwa na Yaƙin Neman Zaɓen ADC, ya fitar, Atiku ya ce lokacin da aka yanke hukuncin yana da abin lura.
Ya ce an yanke hukuncin ne kwana ɗaya kacal bayan dimbin jama’a sun fito a Sakoto domin tarbarsa da halartar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC.
“Al’ummar Sakoto sun fito dubbai saboda suna son sauyi, kuma sun yi imani da alƙawarinmu na dawo da sauƙin rayuwa. Abin da muka gani a can ba komai ba ne face farkon abin da ke tafe. Al’ummar Kebbi ma za su bayyana ra’ayinsu, kuma saƙonmu zai ci gaba da isa ga ‘yan Najeriya a faɗin ƙasar,” in ji Atiku.
“Na yi imanin cewa waɗanda ke wannan zagon kasa sun saka Nafiu-Bala Gombe, wanda shi ma ɗan Arewa ne, ya yi musu wannan aiki ta hanyar amfani da kotu domin hana ni shiga takara. Amma ba za su yi nasara ba, domin goyon bayan da nake samu bai takaita ga Arewa kaɗai ba.
Ya kuma ce ba su wani ɗar-dar sannan za su ɗaukaka ƙara.
A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke takarar Atiku da kuma shugabancin ɓangaren Sanata David Mark.
Kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takarar ADC haramtaccen kwamiti ne.