Daga Auwal Hussain Dukawuya
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya roki gwamnatin tarayya da ta rage kudin aikin Hajjin bana, duba da irin kalubalen da ‘yan kasa ke fuskanta na tattalin arziki.
Gwamnan ya yi wannan roko ne a yayin wani taron da hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta shirya domin mayar wa alhazai kudaden da gwamnatin Saudiyya ta bayar sakamakon matsalar wutar lantarki a lokacin gudanar da aikin Hajjin 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin.
Gwamnan ya kuma yaba wa kokarin gwamnatin Saudiyya kan wannan karamci da ta nuna wurin kulawa ga bil’adama.
Abba ya yi alkawarin aika wasikar godiya ga gwamnatin Saudiyya ta ofishin jakadancinsu dake jihar Kano.
Ya kuma nuna godiya ga hukumar alhazai ta kasa bisa tsantseni da fara biyan kudin akan lokaci.
Gwamnan ya bayyana jin dadinsa kan kokarin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano wurin gudanar da aikin Hajji cikin nasara wanda aka amince da shi a matsayin mafi inganci a kasar nan. Ya kuma bukace su su ci gaba da aiki mai kyau a nan gaba.
Gwamnan ya bayyana cewa ya ziyarci kasar Saudiyya a makonnin da suka gabata domin gudanar da aikin Umrah, sannan kuma ya fara shirye-shiryen aikin Hajji na gaba da kansa domin gano wuraren da Hukumar ke bukatar agajin gwamnati
A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda shi ne jagoran alhazan Kano na shekarar 2024 ya yaba da irin tallafin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa alhazai kafin da lokacin da kuma bayan kammala aikin hajji.
Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Dan Baffa ya ce jimillar kudaden da aka mayar wa jihar ta hannun hukumar alhazai ta kasa domin rabawa Alhazan da suka yi aikin hajjin 2023 Naira miliyan 375.