Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa saƙon ta’aziyya ga tsohon Shugaban Hukumar shigi da fici ta Najeriya kuma mamallakin tashoshin talabijin da radio na MUHASA Muhammad Babandede bisa rashin mahaifiyar sa da yayi a ranar Alhamis.
Muhmmad Babandede ya rasa mahaifiyarsa Hajiya Hajara mai shekaru 90 a ranar Alhamis bayan rashin lafiya da tayi a asibitin Malam Aminu Kano.
Cikin saƙon da ya fitar ta bakin mai magana da yawun sa Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Abba ya bayyana Marigayiya Hajiya Hajara a matsayin mace mai tsoron Allah da kiyaye iyakokin addinin musulunci.
- An Yi Jana’izar Mahaifiyar Muhammad Babandede
- Najeriya Na Iya Samun Tiriliyan 1 Duk Wata A Noman Zogale – Dokta Michael
Gwamna Abba ya kuma jinjinawa tsohon Shugaban Hukumar na shigi da fici Muhammad Babandede bisa irin namijin Kokorin da yayi a lokacin da yake shugabancin hukumar.
A ƙarshe yayi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya kuma bashi ikon jure wannan babban rashin.