Kungiyar manoma da hada-hadar zogale ta Najeriya ta bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta shigar da ‘yan kasa miliyan 50 marasa aikin yi harkar noman zogale za a rika samun kimanin Tiriliyan guda a duk wata.
Shugaban kungiyar ta manoman zogale a Najeriya Dokta Michael Ashimashiga ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja.
Dokta Ashimashiga ya ce, gwamnatin tarayya za ta samu wannan tagomashi ne idan ta tallafa wa manoma da ingantattun iri da takin zamani da sauran kayan aiki.
“Manoman zogale za su iya rika samar da kusan dala biliyan 3.750 a kowane wata idan gwamnatin tarayya ta saka hannu a noman.
“Idan da gwamnatin za ta saka dala miliyan 650 a kowane wata, wurin tallafawa manoman zolgale mutum miliyan 50, to tabbas a duk wata za ta rika samun kimanin Tiriliyan guda aduk wata.
- Yadda Aka Tilastawa ‘Yanwasan Man City Yin Bacci a Tsaye Har Tsawon Kwanaki Biyu.
- Danwasan Super Eagles Osinhem Yayi Rabon Abinci da Keke Napep ga Al’ummar Jihar Legas Abikin Kirsimeti.
Ashimashiga ya ce da Najeriya za ta yi amfani da kasar noman da take da shi da al’ummar da ke kasar yadda ya dace to tabbas ba za ta rika cin bashi ba.
“Duk kasar da ta bada himma wurin taimakawa ‘yan kasarta ko ma’aikatanta ba za ta rika cin bashi wurin gine-gine ba”
Ashimashiga ya jaddada cewa tallafawa ‘yan kasa su shiga harkar noman zogale zai taimaka matuka wajen magance matsalar karancin abinci da tattalin arziki.
Ya ce kungiyar su na da sha’awar a bai wa tsarin rancen kudin noma muhimmanci kamar yadda jaridar agroclimatenews ta bayyana