Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka ta ayyana ƙyandar biri a matsayin cuta mai matuƙar haɗari, bayan ɓullar sabon nau’in cutar da ke yaɗuwa cikin sauri.
Cutar na ƙara yaɗuwa cikin sauri a bana, tun bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Tun daga farkon shekarar nan, rahotanni sun tabbatar da cewa mutum 118 a jihohi 28 daga cikin 36, da kuma Abuja ne suka kamu da cutar a Najeriya, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta sanar.
Hukumar yaki da bazuwar cutuka ta Najeriya ta ce, a wannan shekara daga 27 ga watan Oktoba, , akwai mutane 1,442 da a ke zargin sun kamu da cutar.
Cibiyar CDC, ta ce an samu mutum dubu 14, 500 da suka kamu da cutar ƙyandar biri, sannan akwai mutum fiye da dari 450 da suka mutu sakamakon cutar a tsakanin farkon shekarar 2024.
Hakan ya nuna cewa an samu ƙaruwar kashi 160 na masu cutar, sannan waɗanda suka mutu kuma sun ƙaru da kashi 19 ciki 100 idan aka kwatanta da a shekarar 2023.
Yayin da kashi 96 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ta ƙyandar biri ke a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar kongo, cutar na yaɗuwa zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Burundi da Kenya da Najeriya da Rwanda da kuma Uganda.
Mene ne alamomin cutar ƙyandar biri?
Alamomin farko sun haɗar da zazzabi da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da kuma ciwon gaɓoɓi. da kuraje duk jiki harda tafukan hannaye, da karanje, kuzahari.
Ƙurajen wanda ke da ƙaiƙayi sosai ko kuma zafi, na sauyawa a hankali su zama maruru, daga na sai su fashe.
Ƙurajen na zama a jikin mutum tsawon makonni biyu ko uku, daga nan sai su washe.
To amma idan cutar ta yi tsanani ƙurajen kan yaɗu zuwa dukkan jikin mutum musamman baki da idanu da kuma gaban mutum.
Yawanci ana samun cutar ne a tsakanin mutanen da suke yawan mu’amala da masu cutar, da masu alamomin cutar.
Masana sun bada shawarar a riƙa kaucewa alaƙa ta ƙut da ƙut da duk wanda ke da cutar, sannan a riƙa wanke hannaye da sabulu da ruwa idan akwai cutar a gida ko unguwa ko kuma garin da aka samu bullar cutar.
Abu na biyu kuma ga waɗanda ke da cutar to su killace kansu daga shiga mutane har sai sun warke.
sannan ga wanda ya warke daga cutar idan zai yi jima’i to ya yi rinƙa amfani da kororon roba har sai ya yi makonni 12 da warkewa, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Hanyoyin kare kai
Za’a iya shawo kan ɓarkewar cutar ƙyandar biri ta hanyar yaɗuwar cutar musamman yin rigakafi.
Akwai alluran rigakafi uku da ake yi, to amma ana yi wa mutanen da ke da yiwuwar kamuwa da cutar ne rigakafin ko kuma waɗanda suka yi alaƙa ta ƙut da kut ga masu cutar.
A yau Litinin 18 ga Nuwamba ne za a fara allurar riga-kafin ƙyandar biri a wasu jihohi bakwai a Najeriya. Wanda hakan zai sa ƙasar ta zama ta uku da za ta yi riga-kafin bayan Rwanda da Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya za ta yi riga-kafin a kan cutar ta ƙyandar biri bayan ɓarkewarta.
Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta ce za a fi mayar da hankali ne a kan ma’iakatan lafiya da sauran rukunan jama’a da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
A watan Agusta, Najeriya ta karɓi allurarn riga-kafin na farko da aka bai wa Afirka, wanda kuma a wannan watan ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya
Amurka ta bai wa Najeriya kwalaban allurar sanfurin Jynneos (MVA), 10,000.
Dokta Umar Iliyas masanin fanin cututtuka daga asibitin koyarwa na malam Aminu kano yace rashin karban rikakafin kyandar birin ba karamin ila zata yiwa al’umma ba.
Dokta Umar yayi kira ga al’umma da su karbi wannan rigakafin da za’a farayi a fadin kasar nan, inda yace akwai rigakafin na masu cutar da kuma rigakafin ga wadanda ba su kamu da cutar ba. Inda yace rigakafin zata taimaka matuka gurin dakele yaduwar cutar cikin al’umma da ma kasar baki daya.