Ministan Maikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ya zargi Isra’ila da kokarin raba Falasdinawa daga kasarsu.
Wadannan kalama na na zuwa ne bayan da aka karkatar da akalar wani jirgin saman fasinja zuwa Johanesburg dauke da Falasdinawa 153 da kuma tun farko ya nufi kudancin birnin Eilat na Isra’ila ne.
Wata kungiyar bayar da agaji dai ce ta tsara tafiyar, kuma Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ba ta da masaniyar kome akan lamarin sai a ranar Alhamis da suka sauka.
Ministan harkokin wajen Afrika ta Kudun Ronald Lamola, ya ce matakin na da nasaba da wata boyayyar manufar neman share Falasdinawa ne daga Gaza inda ya ce ba za su lamunci wannan cin zaliba.

