Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta lashe zaben shugabancin Kungiyar mata ‘yan jarida wato NAWOJ ta kasa, wanda aka gudanar a Birini taraiyya Abuja.
Aisha Bura ta bayyana farin cikinta game da lashe zaben da tayi, inda ta ce za tayi duk mai yuwa wajen ganin tayi aiki da zai kawo ci gaba a wanan kungiyar mata ‘yan jarida NAWOJ.
Itama ana ta bangaren ‘yar takarar Sakatare kungiyar mata ‘yan jarida NAWOJ ta kasa Amma reshen jahar Kano Hajiya Wasila Ladan tayi godiya ga Allah bisa wanan zabe da lashe .
Sannan ta Kara da cewa gwamnatinsu zasu kwatanta adalci tare da sauke Nauyin da Allah ya Dora musu.