Akanta Janar ta Nijeriya, Dakta Oluwatoyin Madein, ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda take mayar da martani game da wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ma’aikatar ayyukan jinkai ta nemi a biya kudin tallafi ga wasu ‘yan kasar nan da ke fama da da talauci.
A bayanin da ta yi, ta ce ana ware wa kowacce hukuma kasonta a cikin kasafin kudi kuma kowace hukuma ita ke da hakkin aiwatar da wadannan ayyuka da kuma biyan kudin ayyukanta.
Dakta Oluwatoyin ta ce duk da cewa ofishinta ya samu bukatar biyan wadannan kudade daga ma’aikatar Jin-ƙai, amma ba a biya ba, inda ta ce sun bai wa ma’aikatar shawara kan irin matakan da ya kamata ta dauka domin ganin an biya ta wadancan kudade.
A cewar Akantar kamata ya yi a tura wa wadanda za su amfana da tallafin zuwa asusun bankunansu, amma ba wani mutum ɗaya ba.