Home » Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta ta bunkasa ilimi

Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta ta bunkasa ilimi

by Anas Dansalma
0 comment
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimin jihar Alhaji Umar

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin ci gaba da haɓaka ɓangaren Ilimin jihar.

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimin jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa, wanda yace gwamnatin Kano ba za ta gaza ba wajen bunƙasa ilimi a jihar domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa.

 

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2024 wanda aka gudanar a harabar shalkwatar ilimin bai ɗaya na jihar Kano a jiya Laraba.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa an ware wa ɓangaren ilimi kaso 29.7 cikin 100 a kasafin kuɗin wannan shekara da muke ciki a matsayin wani yunƙuri na ƙara inganta ilimi a jihar.

 

Da yake mana ƙarin haske a yau a yayin wata ziyara da ya kai ofishin Asusun Tallafa Wa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF,  a nan Kano, kwamishinan ilimi ya bayanna mana maƙasudin ziyarar tasa da cewa.

Kwamishinan ilimin ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano ta gyara motocin bas sama da 60 domin sauƙaƙa wa ɗalibai zuwa makarantunsu tare da tabbatar da cewa an samar da kayayyakin koyarwa ga malamai da kuma tada komaɗar wasu daga cikin makarantun da ke faɗin jihar.

 

Sannan ya ce gwamnati ta kashe Naira miliyan 740 wajen biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar NECO na NBAIS a faɗin jihar a yayin da ya ce tuni gwamnati ta fara shirin biyan kuɗaɗen jarrabawar wannan shekarar domin tabbabar da samar da ilimi a jihar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?