Akwai ‘Yan Siyasar Dake Taimakawa Masu Zanga-Zanga – Kashim Shettima

Kashim Sherttima Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na da niyyar kawowa al’umma sauki a halin kuncin da suke ciki. Sai dai yace akwai mutanen da ke kawo musu cikas wajen wannan kokari.

Shetttima ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis lokacin da yake ganawa da yan jarida a birnin tarayyar Abuja

“Da yardar Allah wannan gwamnati na kawo tsare-tsare na taimakawa al’ummar kasar nan.”

Mataimakin shugaban Najeriyar, ya  kara da cewa gwamnati a kokarin ta na shawo kan halin kunci da tsadar abinci da ake fama da ita, sun ɗauki matakai da suka haɗa da fito da ton dubu 42 na hatsi domin tallafa wa al’ummar ƙasar da kuma ƙarin mafi ƙarancin albashi daga dubu 30 zuwa naira dubu 70.

Shettimma ya kara da cewa, “ muna da niyyar samawa matasa aikin yi, mun kawo tallafin karatu, wanda ba sai kasan wani ba, kuma Insha Allahu zamu samawa matasan Arewa aikin yi.

Shettima ya ce sun san halin da matasan suke ciki, kuma nan ba da jimawa ba za su yi taron gwamnoni da attajirai da masu ruwa da tsaki na arewacin Najeriya domin fitar da wani tsari da zai taimaka wa yankin.

“Taron da za mu yi ba na shan shayi bane, da cin kaji, muna son a gani a ƙasa ne, kowane attajiri da yake son ya yi taimako ya faɗi me zai kawo, kuma na yi imanin za su taimaka, za kuma mu gayyaci Rabi’u Musa Kwankwaso.” a cewar Shettima.

Yanzu lokaci ne da zamu hada kai ba tare da nuna banbancin siyasa, kabila ko addini ba. Dole mu hada kanmu domin ceto kasar mu daga halin da take ciki.

 

Post masu alaƙa

Ɗalibai makafi 135 sun rubuta jarrabawar JAMB a Kano

Kotun Ƙoli ta ɗage Shari’ar kujerar Sarkin Kano zuwa 2027

Babbar alkalin Kano ta rantsar da sabbin alkalan kotunan shari’a su 30