Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Rundunar yan sandan Nijeriya shiyya ta daya dake Kano, Zone Kano ta kama mutane biyar da ake zargi da kwaikwayar wani mai maganin gargajiya da sayar da jabun magunguna da sunansa.

Kakakin rundunar shiyya, DSP , Abdullahi Hussaini, ya ce an kama wadanda ake zargin bayan ƙorafin Dakta Abdulwahab Abubakar Goni Bauchi, shugaban wani asibitin magungunan gargajiya da na musulunci da ke Bauchi, wanda ya zargi mutanen da amfani da sunansa da bayanan kasuwancinsa wajen yaudarar jama’a.

Rundunar ta ce ana zargin waɗanda aka kama da karɓar kuɗin jama’a ba tare da kai musu magungunan da suka saya ba, tare da sayar da jabun magungun bogi da ka iya cutar da lafiya.

Waɗanda aka kama sun hada da Muhammad Usman, Husaini Kabir, Hassan Kabir, Suleiman Salihu da Nura Garba.

Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya mai kula
da shiyya ta daya, AIG Garba Ahmed ya gargadi jama’a da su tabbatar da sahihancin magunguna da masu sayar da su kafin biyan kuɗi, musamman a kafafen sada zumunta.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano sauran waɗanda ake zargin suna da hannu, kuma duk wanda aka tabbatar da laifinsa zai fuskanci hukunci bisa doka.

Post masu alaƙa

Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe

Zaɓen 2027: CP Bakori ya gargaɗi jami’an ’yan sanda kan tsoma baki a siyasa.

Kamfanin Tianneng ya ƙaddamar da sabbin babura masu kafa biyu da masu kafa uku, waɗanda ke amfani da wutar lantarki, a wani biki da ya gudana a nan Kano.