kwamitin Abinci a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargadin cewar akwai yiwuwar samun matsananciyar yunwa a wasu ƙasashe 16 cikin watanni masu zuwa.
Hukumomin sun ce yankunan Sudan ta Kudu da Ƙasar Mali da Haiti da yankunan Falasɗinu su ne kan gaba wajen fuskantar wannan matsala.
Ƙasashe irin su Najeriya na daga cikin ƙasashen da ake hasashen za’a samu matsananciyar yunwa.
Ƙasar Yemen da Myanmar da Syria da Lebanon da Chadi da Mozambique duk suna cikin fargaba ta fuskantar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa.
Rikice -rikice musamman a gabas ta tsakiya na daga cikin dalilan da za su haifar da ƙarancin abinci, a cewar hukumar, wanda hakan zai haifar da yunwa wadda mai tsanani.
Ayyukan yan bindiga a ƙasashe irin su Najeriya na daga cikin musabbabin da ba’a iya noma da za ta wadaci al’umma, Hukumar ta ƙara da cewa matuƙar ba’a ɗauki matakan da suka dace ba to za’a fuskanci matsala.