Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa.
Wannan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a daren ranar Lahadi.
“Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, yanzu muke samun labarin rasuwar Malam Nata’ala, Allah Ya gafarta masa, Allah Ya sa jinya ta zama kaffara.”
Jarumin ya jima a kwance yana fama da rashin lafiya, inda ya sha fitowa a cikin wasu faifan bidiyo yana neman taimakon jama’a kan rashin lafiyar da yake fama da ita.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin yi wa marigayin magani.
Hakazalika, a baya Malam Nata’ala ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar Nijar, ya taimaka masa da kuɗi kimanin Naira miliyan 27 domin ya ci gaba da neman magani, bayan ya nemi taimakon jama’ar gari.
An haifi Malam Nata’ala a ranar 15 ga watan Agustan 1967 a ƙauyen Damboa-Rijiya a garin Potiskum da ke Jihar Yobe.
Jarumin ya rasu a ranar Lahadi 2 ga watan Nuwamba, 2025, yana da shekaru 58, sannan ya bar mata uku da ’ya’ya 10.