Fursunan Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Ya Tsere Daga Gidan Yari A Yobe

Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe.

Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa  Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa.

DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da su taimaka da bayanai da za su taimaka wajen sake kama shi.

Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su kusanci fursunan da ya tsere, domin hakan na iya zama hatsari.

“Domin kare lafiyarku, idan kuka ga wani da kuke zargi shi ne, ku sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa ko gidan gyaran hali, ko kuma ku kira lambar 08038452982,” in ji sanarwar.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro