Allah Ya yi wa Mai martaba Ohinoyi na kasar Ebira, Alhaji Ado Ibrahim rasuwa wanda har ila yau shi ne mataimakin shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na kasa,
Dokta Ado Ibrahim ya kasance shahararren dan kasuwa wanda ya shafe yawancin rayuwarsa a jahar Lagas kafin ya zama Ohinoyi na kasar Ebira. Ya hau kujerar sarautar Ohinoyi na kasar Ebira bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori na gidan Oziada a shekarar 1997.
An haifi marigayi sarkin ne a ranar 7 ga watan Fabrairun shekarar 1929. Ya yi karatun boko da na addini, ya rasu yana da shekaru 94. Za a yi jana’izarsa a yau lahadi 29 ga watan Oktoba, a fadarsa da ke birnin Okene, a Jihar Kogi.