Tun bayan faruwar ambaliyar ruwa da tayi sanadiyar rasuwar mutane aƙalla 95 tare da raba wasu da muhallan su, ana cigaba da aikin ceto a garin Valeancia dake ƙasar Sifaniya.
Lamarin ya faru a ranar Laraba 30 ga watan Oktoba na shekarar 2024, inda aka shafe awanni shida ana tafka ruwa babu ƙaƙƙautawa. Wannan ita ce ambaliya mafi muni da aka gani a kasar ta Sifaniya.
Zuwa yanzu dai waɗanda suka rasu sun kai aƙalla mutum 95, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ɗan Burtaniya mai shekara 71 bayan an ceto shi a gidansa da ke Alhaurin de la Torre a garin Malaga.
Kawo yanzu dai ruwan ya tsagaita, amma firaiministan ƙasar Pedro Sanchez, ya ce akwai buƙatar mazauna yankin su ɗan dakata a tabbatar da tsayawar ambaliyar.
Hukumomi dai a ƙasar sun ce har yanzu ba a tantance haƙiƙanin mutane nawa suke ɓace ba a sanadiyar ambaliyar.
Mutane da yawa sun yi asarar dukiyoyin su da suka haɗa ababen hawa da gidaje dadai sauransu.