Majalisar ɗinkin Duniya ta ware ranar 31 ga watan Oktoban ko wace shekara a matsayin ranar birane ta duniya.
Maƙasudin ranar shine jawo hankulan hukumomi game da yadda za’a inganta da kuma ƙawata birane, tare da shigar da matasa cikin harkokin tafiyar da biranen.
Ranar tana ƙoƙarin nusar da mutane muhimmancin samar da nagartattun tsare-tsare da za su kawo gyara da cigaba mai ɗorewa ta hanyar da za’a samu ingantattun birane.
- Alh. Muhammad Babandede Ya Zama Jagora A Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Ƙasa
- Sarakunan Gargajiya 19 Sun Yi Murabus A Sokoto
Birane na daga cikin wuraren da ƙasashe ke amfani dasu don samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatoci.
Manyan biranen duniya suna amfani da biranen su don alkinta abubuwa na tarihi da kuma al’ada wanda hakan yake zamar musu hanyar kuɗin shiga.