Cibiyar Kasafin Kudin Lafiya Ta Afirka (AHBN) Ta Jaddada Bukatar Samar Da kudade A Shirye-shiryen Rigakafi A Kano.
Cibiyar Kasafin kudi Lafiya ta Afirka (AHBN) a Nijeriya ta jaddada bukatar ƙara ba da kuɗi da kuma sakin kuɗi da wuri don shirye-shiryen alluran riga kafi a Jihar Kano. Dr. Musa Muhammad Bello, Wakilin AHBN na Jihar Kano , ya yi wannan kira yayin wani taron manema labarai da rarraba katin sakamako a Asibitin […]