Mazauna unguwar Yalwa ƴan Haya da ke ƙaramar hukumar Dala a Kano, sun bayyana cewar har yanzu suna cikin firgici tun bayan da suka yi zargin wasu jami’an tsaro sun shiga unguwar su sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Mazauna yankin sun ce al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka zargi jami’an tsaron ƴan sanda da harbin mutane biyar, biyo bayan zargin wasu dandazon matasa sun jefi jami’an da ke aiki a unguwar Jakara, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutum ɗaya.
Wasu matasa a yankin sun ce, da safiyar ranar Talata 11 ga watan Nuwamba, 2025, wani matashi ya ƙara rasuwa, wanda ya zama mutum na biyu kenan da su ka rasu, baya ga wasu mutane uku da suke asibiti don samun kulawar likitoci.
- Kotu Ta Umarci Kwamandan Sojoji Ya Kai Mata Sojan Da Ake Zargi Da Halaka Dan KAROTA
- Gwamnatin Kaduna Ta Ce Shekaru 2 Da Rabi Ba A Samu Ricikin Addini Ko Kabilanci Ba
Shima wani mazaunin yankin ya magantu, inda ya yi kira ga gwamnatin Kano, da kwamishinan ƴan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori, da su shiga cikin lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace akan al’amarin.
A cewar sa, “Ko a daren ranar Asabar da ta gabata muna tare da guda daga cikin waɗanda su ka rasu bayan da ya kwana a ɗakina, na dawo daga makaranta na tarar da faruwar lamarin wanda tuni aka yi jana’izar aminina, in ji matashin.”
Barista Yusuf Mu’azu Sani, shi ne lauyan iyalan waɗanda al’amarin ya faru da su, ya ce matuƙar ba a yi adalci akan batun ba za su garzaya kotun domin nemawa waɗanda lamarin ya shafa hakƙinsu.
A ranar litinin din data gabata wakilin mu ya tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, kan zargin da ake yiwa jami’an yan sandan, inda ya bayyana masa cewa zai bincika lamarin.