An kashe fiye da ƴan bindiga 200 a jihar Kogi

Hukumomin Najeriya sun ce jami’an tsaro sun kashe fiye da ‘yanbindiga 200 a wani “gaggarumin samamen hadin gwiwa” da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro a ƙasar. ‘Yansanda sun kuma kama wasu da ba a fayyace adadinsu […]

Read more

An daƙile wani harin ’yan bindiga a Gombe

Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile wani harin ’yan bindiga da ake zargi an yi yunƙurin kaiwa garin Guda Lamido, da ke yankin Kashere a ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asubahin ranar Talata, 13 ga Janairu, 2026, bayan da aka samu rahoton cewa wasu ’yan […]

Read more

Gobara ta ƙone ajujuwa da ɗakin taro a GSSS Jalingo

Gobara ta ƙone ajujuwa da ɗakunan ajiya da kuma babban ɗakin taro a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSS) da ke Jalingo, a Jihar Taraba. Gobarar ta lalata kusan dukkan ajujuwan makarantar da littattafan karatu, da babban ɗakin jarabawa, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin karatu a makarantar. Ana zargin gobarar ta fara ne […]

Read more

Magoya bayan Kwankwaso sun ƙi halartar taron Gwamna Abba

A daidai lokacin da raɗe-raɗen sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ke ci gaba da ɗaukar hankali a Kano, an sake ganin wata sabuwar ɓarakar da ke nuna akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamnan da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. A ƙarshen mako, wasu manyan magoya bayan Kwankwaso sun ƙaurace […]

Read more

An jibge motocin yaƙi a Gidan Gwamnatin Kano

An tsaurara ƙarin jami’an tsaro a gidan Gwamnatin Jihar Kano a safiyar Litinin a yayin da ake dakon sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf. Wakilinmu ya lura cewa an girke ƙarin ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS a babbar ƙofar shiga da wasu muhimman wurare a gidan gwamnatin. Sojoji sun ceto fasinjojin da […]

Read more