Amurka ta kai wa Najeriya tallafin ‘kayan aikin soji’

Rundunar sojin Amurka da ke gudanar da aikinta a nahiyar Afirka ta sanar da bai wa Najeriya kayan aiki bunƙasa yaƙi da matsalar tsaro.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, yau Talata.

Sanarwar ta ce “dakarun Amurka sun sauke muhimman kayan aikin soji ga abokan huldarmu na Najeriya a Abuja.

“Wannan tallafi zai taimaka wa Najeriya a wajen ayyukanta, kuma hakan ya ƙara jaddada alaƙar tsaro da ke tsakanin mu,” a cewar sanarwar.

Haka kuma sanarwar na ƙunshe da hoton wani jirgin dakon kaya da ƙofarsa a buɗe, yayin da za a iya ganin wasu kaya jibge a kusa da jirgin.

Najeriya na fama da matsalar tsaro a yankunanta daban-daban: waɗanda suka hada da matsalar ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, da ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewa maso gabashin ƙasar da arewa ta tsakiya, sai kuma ƴan aware a kudu maso gabashin ƙasar.

A ranar 25 ga watan Disamban 2025 ne Amurka ta ce ta kai hari kan ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto da ke Najeriya.

Duk da babu cikakken bayani kan tasirin harin, amma shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren “suna da ƙarfi da haɗari”.

Post masu alaƙa

Rukunin farko na ‘yan Najeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu zai isa ƙasar ranar Alhamis

Gwamnatin Sakkwato ta tallafa wa Alhazai 47 da suka ɓatar da kuɗin guzurinsu

An kammala shirye-shiryen tabbatar da tsaro a zaɓen cike gurbin ɗan majalissar wakilan Dawakin Kudu/Warawa a Kano.