Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli a Jihar Kano ta rufe gidan mai, gidajen wanka da wajen sayar da nama na ƴan gayu saboda karya dokokin tsaftar muhalli a wasu sassan jihar.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kwashe shara ta Kano REMASAB, Malam Abubakar Ahmad ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa kotun ta rufe gidan mai na M.R.S da ke kan titin Katsina bayan samunsa da laifin rashin tsafta a harabar wurin, rashin cire ciyayi da kuma rashin tanadar da wuraren zuba shara.
Haka kuma an ci tarar shaguna biyu da ke kan titin Katsina, yayin da aka hukunta gidajen wanka biyu a tashar mota ta Malam Kato saboda rashin tsafta, lalacewar gine-gine da kuma rashin wuraren zubar da shara.
A Kofar Dawanau kuwa, kotun ta rufe wajen sayar da nama irin na ƴan gayun nan wato ba mai tukuba ta gargajiya ba mai suna Yack’s Suya Spot tare da wasu gidajen wanka biyu saboda karya dokokin tsaftar muhalli.