An daƙile wani harin ’yan bindiga a Gombe

Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile wani harin ’yan bindiga da ake zargi an yi yunƙurin kaiwa garin Guda Lamido, da ke yankin Kashere a ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asubahin ranar Talata, 13 ga Janairu, 2026, bayan da aka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga da dama sun yi yunƙurin kutsa kai cikin ƙauyen domin kai hari.

Bayan samun rahoton ne jami’an rundunar ’yan sanda tare da ’yan sintiri da mafarauta suka yi gaggawar kai ɗauki wurin, inda suka tari hanzarin maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa dajin da ke kusa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata a yayin arangamar.

Ya ƙara da cewa yanzu haka hankalin jama’a ya kwanta a yayin da al’amuran yau da kullum suka kankama.

Kazalika, DSP Buhari ya ce an ƙara tsaurara aikin sintiri da sa ido a yankin da maƙwabtan ƙauyukan domin tabbatar da tsaro.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya jinjina wa ƙwazon jami’an tsaron suka nuna, tare da yaba wa gudunmawar ’yan sintiri da mafarauta, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da taka rawar gani wajen kare al’umma.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ’yan sanda ta ƙuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka a jihar.

Post masu alaƙa

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe