Gwamnonin Arewa za su kafa gidauniyar yaƙi da matsalar tsaro a yankin
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya sun amince da kafa wata gidauniya domin samar da kuɗin yaƙi da matsalar tsaron da ke addabar yankin. Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun ce sun amince kowace jiha ta bayar da naira biliyan ɗaya cikin asusun. Sai dai gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su […]