Gwamnan Kano ya guji siyasantar da matsalar tsaron jiharmu – Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibril ya buƙaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya guji siyasantar da matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta, a maimakon haka ya mayar da hankali wajen magance ɗimbin matsalolin da ya ce na damun Kano.

Cikin wata sanarwa da Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, ya ce yana martani ne kan zargin da ya ce gwamnatin Kano ta yi masa na yin wasu kalamai da ka iya ta’azzara matsalar tsaron jihar.

Sanarwar ta musanta iƙirarin gwamnatin, inda ta ƙalubalanci gwamnatin Kano ta bayyana sautin murya na inda Sanatan ya yi kalaman.

Sanata Barau ya ce matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta ciki har da hare-haren ƴanbindiga a Kano a baya-bayan nan, na buƙatar haɗin kan kowa da aiki tare domin maganceta.

“Abin mamaki ne yadda gwamnatin jihar Kano ke siyasantar da tsaro ta hanyar ƙirƙirar ƙarairayi domin ɓata wa mataimakin shugaban majalisar dattawa suna”, in ji sanarwar.

”Babu inda Sanata Barau ya furta wasu kalamai da ke zagon-ƙasa ga sha’anin tsaro a ƙasar nan, a maimakon haka ma a kullum yana kan gaba wajen samar da hanyoyin magance matsalar”, kamar yada sanarwar ta yi ƙarin haske.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu