Ƙananan Hukomomin Kano 44 sun kare kasafin kuɗin 2026

Kwamitin ƙananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Kano, ya zauna da shugabannin ƙananan hukumomi 44, domin su kare kasafin kuɗin su na 2026 da su ka mika.

Kwamitin wanda aka raba zuwa gida shida, ya gana da shugabannin ƙananan hukumomi daban-daban.

Hakaazalika bayan kammala kare kasafin kuɗin na su a gaban majalisar, shugabannin sun bayyana cewa, kasafin kuɗin na su na 2026, zai mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin Ilmi da lafiya sai kuma ayyukan raya kasa.

Rahotanni na cewa ƙananan hukumomin sun gabatarwa majalisar adadin kasafin kuɗin da ya kai kimanin sama da Biliyan Goma kowace ƙaramar hukuma.

Post masu alaƙa

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa