Amurka Ta Amince Kasashen Turai Su Bai Wa Ukraine Wani Jirgin Yaƙi

Amurka ta ce za ta ƙyale ƙawayenta na Nahiyar Turai su bai wa Ukraine jirgin yaƙin da ta ƙera na F-16.

Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, Jake Sullivan, ya ce Shugaba Joe Biden ya faɗa wa taron ƙasashen  mafiya girman tattalin arziki a duniya da akafi sani da  G7 game da matakin yayin taron da suke gudanarwa a Japan yanzu haka.

Sojojin Amurka za su bai wa na Ukraine horo kan yadda za su yi amfani da jiragen .

Ukraine ta daɗe tana neman manyan makamai na zamani daga ƙawayen nata, kuma Shugaba Volodymyr Zelensky ya yabi matakin da cewa mai cike da tarihi.

Ƙasashen da suka mallaki irin waɗannan makamai ko jirage ba za su iya sayarwa ko kuma kai su wata ƙasa ba sai da amincewar Amurka.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro