Rundunar yan sandan Kano ta kama kasurgumin dan Daba da ake zargi da garkuwa da Yaro mai shekaru 9

Rundunar yan Sandan Jihar Kano ta ce ta cafke wani matashi mai suna Abubakar Isma’il, wanda aka fi sani da Sankolo, bisa zargin aikata daba da kuma sace wani yaro mai shekaru tara.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke Sankolo mai shekaru 22 a unguwar Rimin Kebbe a ranar 6 ga Nuwamba, bayan samun bayanan sirri da suka biyo bayan kama wani da ake zargi da aikata laifuka tare da shi, Umar Usman, wanda aka fi sani da Ta’ambo.

Ya ce ana zargin Sankolo da hannu wajen sace Ubaidu Sammani, ɗan Alhaji Sammani, a ranar 3 ga Yuli, 2026, lamarin da ya sa aka sanya shi cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo.

A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa hannu a wasu ayyukan daba da kwacen wayoyin salula a Rimin Kebbe da kewaye, inda ake zarginsa da jagorantar hare-hare da tsoratar da mazauna yankin.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin suna tare da shi da kuma gano makaman da ake amfani da su wajen aikata laifuka.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da kira ga al’umma da su riƙa kai wa ’yan sanda bayanan sirri domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka.

Post masu alaƙa

Ana fargabar mutum daya ya rasu, wasu biyar sun jikkata yayin da yan jagaliya suka tarwatsa magoya bayan NDC a jihar Delta. 

NOA ta taya kungiyar kwallon kafa ta mata ta yan kasa da shekaru 17 nasarar lashe gasar kofin duniya.

Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Kano ya ziyarci CP Ibrahim Adamu Bakori.